• Yarjejeniyar Nukiliya : Iran Za Ta Dawo Da Shirinta Na Nukiliya, Idan Amurka Ta Janye

Ministan harkokin wajen Jamhuriya Musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta koma kan shirinta na nukiliya, idan har Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da ita.

Mista Zarif, ya bayyana hakan ne ga 'yan jarida a birnin New York, inda yake cewa tabbas Iran zata komawa shirinta na nukiliya da karfi, idan har Amurka ta janye daga yarjejeniyar.

Ministan harkokin wajen Iran din, ya jaddada cewa kasarsa bata neman mallakar makamin nukiliya, amma martanin da zata mayar shi ne komawa ga shirinta na nukiliya da karfinta.

Shugaba Trump na Amurka dai ya yi barazanar janye kasarsa daga yarjejeniyar, inda ya baiwa kasashen Turai wa'adin har zuwa ranar 12 ga watan Mayu domin su gyara yarjejeniyar da ya danganta da mai cike da kura kurai. 

Tags

Apr 22, 2018 11:16 UTC
Ra'ayi