Mayu 20, 2018 07:56 UTC
  • Iran Ta Ci Nasara A Harakokin Siyasar Waje Da Kuma kalubalantar Masu Mugun Nufi

A yayin da yake ganawa da wasu matasan kasar a daren jiya asabar, Shugaban Jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya ce Kasarsa ta ci nasara a harakokin siysarta ta waje da kuma tsayin wajen kalubalantar masu mugun nufi.

Dakta Hasan Rauhani ya ce bukatar Amurka, janyewar kasar Iran daga yarjejjeniyar Nukiliyar da kasar ta cimma tare da manyan kasashen 5+1 bayan da ta janye, wanda hakan zai sanya a kai fayil din kasar  zuwa kwamitin tsaron MDD a sake mayar mata da dukkanin takunkumin da aka kakaba mata a baya sannan kuma a mayar da ita saniyar ware a Duniya, amma wannan makirci da makarkashiya bai ci nasara ba.

Shugaba Ruhani ya kara da cewa a yau Duniya ta bayana matakin Trump na ficewa daga yarjejjeniyar Nukiliyar Iran a matsayin abinda ya sabawa doka, kuma sabanin sulhu da tsaro na Duniya, kuma wannan cin nasara ce ga kasar Iran.

A ranar 8 ga wannan wata ne Shugaba Donal Trump na Amurka ya sanar da fitar kasarsa daga yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiyar Iran tare da manyan kasashe 5+1, bayan da ya zarki Iran din da tayar da hargizi da kuma taimakawa 'yan ta'adda a yankin gabas ta tsakiya.

Tags

Ra'ayi