Mayu 20, 2018 19:00 UTC
  • Zarif: Goyon Bayan Baka Wanda Turawa Suka Bawa Shirin Nukliyar Kasar Iran Bai Wadatar Ba.

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce goyon bayan baka wanda kasashen turai suke wa shirin nukliyar kasar Iran bai wadatar ba

Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta nakalto muhammad Jawad Zarif yana fadar haka a yau Lahadi a lokacinda yake ganawa da tawagar tarayyar turai da take ziyarar aiki a nan tehran. Ministan ya bukaci kasashen na turai su dauki matakan goyon baya a aikace ta hanyar zuba jari a kasar Iran don kyautata tattalin arzikin kasar.

Zarif ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da Miguel Arias ministan makamashi da yanayi na tarayyar Turai da tawagarsa a nan Tehran. Wannan ita ce tawagar tarayyar turai ta farko zuwa kasar Iran tun bayan janyewar Amurka daga yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar yan makonni da suka gabata. Ministan ya kara da cewa akwai kashe guiwa kwarai da jin cewa wasu manya manyan kamfanoni na kasashen Turai suna shirin dakatar da ayyukansu a kasar Iran don jin tsaron takunkuman da Amurka zata dorawa kasar.

A nashi bangaren ministan makamashi na tarayyar Turai ya kara jaddada matsayin kungiyar na ci gaba da mutunta yerjejeniyar.

 

Tags

Ra'ayi