Jun 03, 2018 19:08 UTC
  • Shamkhani Ya Ce: Amurka Ta Wurga Kanta Cikin Damuwa Tare Da Zama Saniyar Ware

Babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Hare-haren wuce gona da irin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila kan yankunan Palasdinawa nade tabarmar kunya da hauka ce bayan rushewar makircin kunna wutan rikicin ta'addanci a kasashen musulmi.

Babban sakataren kwamitin tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ya jaddada cewa: Dawowar zaman lafiya a kasashen Siriya da Iraki wata babbar barazana ce kuma hatsari ga zaman lafiyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila 'yar mamaya saboda hankulan al'ummar musulmi zasu koma kan matsalar Palasdinu.

Shamkhani ya kara da cewa: Bayan da makircin Haramtacciyar kasar Isra'ila da uwar gijiyarta Amurka ya kawo karshe sakamakon murkushe gungun 'yan ta'addan kasa da kasa masu kafirta musulmi a kasashen Siriya da Iraki, hakan ya sanya gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kokarin nade tabarmar kunya da hauka ta hanyar zafafa hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Palasdinu.

Har ila yau babban sakataren kwamitin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: A halin yanzu al'umma da dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya sun kai ga tabbacin cewa babu wani amfani da za a samu a gudanar da zaman tattaunawa da kasar Amurka kan tilastawa haramtacciyar kasar Isra'ila dakatar da munanan manufofinta kan Palasdinu. 

Tags

Ra'ayi