Jun 23, 2018 09:12 UTC
  • Kotun Duniya Za Ta Duba Karar Da Iran Ta Shigar Kan Kudadenta Da Amurka Ta Handame

Babbar kotun duniya ta sanar da cewa za ta fara gudanar da zaman sauraren karar da Iran ta shigar kan handame wasu wasu biliyoyin dalolinta da Amurka ta yi.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne babbar kotun ta duniya ta fitar da bayani da ke tabbatar da cewa, alkalan kotun za su fara gudanar da zama kan karar da Iran tashigar a kan Amurka, dangane da kudinta da Amurka ta rike.

Kasar ta Amurka dai ta rike biliyoyin dalolin kudin na Iran bisa hujjar takunkumin da aka dora mata, kuma bisa ka'ida dole ne Amurka ta mayar mata da kudaden nata bayan da majalisar dinkin duniya ta janye takunkuminta  akan Iran, bayan cimma yarjejeniyar nukiliya, amma Amurka tana ci gaba da yin kememe kan batun.

Tags

Ra'ayi