Jul 01, 2018 17:47 UTC
  • Za Mu Wargaza Shirin Amurka Na Hana Mu Sayar Da Man Fetur Ketare_Iran

Jamhuriya Musulinci ta Iran ta ce za ta wargaza makircin Amurka, na hana ta sayar da man fetur dinta a kasuwannin duniya.

Da yake bayyana hakan a gidan talabijin din kasar, mataimakin shugaban kasar, Eshagh Jahangiri, ya ce zamuyi wani shiri na kawo karshen duk wani makircin Amurka a kan man fetur din Iran, tare da jan kunnen Saudiyya data shiga tafiye tafiyenta.

Mista Jahangiri, ya kara da cewa gwamnatin kasar na da wani shiri, wanda take da yakinin cewa da yardar Allah, zata iya sayar da man fetur dinta yadda take so.

A ranar Talata data gabata ce, gwamnatin Amurka, ta bukaci kasashen China da Indiya, manyan kasashe abokan cikin Iran, dasu dakatar da sayan man fetur din na Iran daga nan zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba, ko kuma su fuskanci jerin takunkumai da Amurkar ta dora wa Iran bayan janyewarta daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Ranar 4 ga watan Nowamba mai zuwa ne, Amurka ta ce takunkumanta kan makamashi zasu fara aiki kan Iran.

Tags

Ra'ayi