Jul 11, 2018 15:53 UTC
  • Tehran Ta Yi Tir Da Kalaman Pompeo Kan Ofisoshin Jakadancinta

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi tir da allawadai da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya furta kan ofisohin jakadancinta, wanda ya zarga da hannu a shirya ayyyukan ta'addanci.

Da yake bayyana hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Bahram Qassemi, ya ce kalaman na Pompeo, abun dariya ne, don kuwa basu da tushe balle makama, wanda kuma a cewarsa kamfe ne na Amurka kamar kulum na nuna kiyaya da kuma bata wa Jamhuriyar Musulinci ta Iran suna.

Mista Qassemi, ya ce tarihi dai ya nuna misalai da yawa na tsoma baki da shishigi da leken asiri da ta'addanci da hadassa fitina da Amurka ke yi a cikin kasashen duniya da dama, wanda hakan kuma ya sabawa huldar diflomatsiyya.

Ya kara da cewa har koda yaushe, ofisohin jakadancin Iran, a sauran kasashen na aiki kafada da kafada da kasashen da take alaka dasu don ci gaba, wanda kuma manufar Amurka shi ne ganin ta ruguza wannan alaka ta tsakanin Iran da abokanta.

 

Tags

Ra'ayi