Jul 11, 2018 15:56 UTC
  • Iran Da Pakistan Sun Cimma yarjejeniyar Bin Tsarin Harajin Kaya Ta Yanar Gizo

An fara aiwatar da yarjejeniyar da Iran da Pakistan suka rattaba wa hannu a kwanakin baya, ta yin aiki da hanyoyi na yanar gizo a kan batun fito a kan iyakokin kasashen biyu, da kuma sauran tsare-tsare da suka danganci harajin kayayyaki.

Ma’aikatar kula da shige da ficen kayayyaki a Iran ta sanar da cewa, an fara yin aiki da wannan tsari tsakanin Iran da Pakistan daga jiya Litinin, wanda hakan zai zama hanya mafi sauri wajen gudanar da ayyukan shigar da kayayyaki ko fitar da su daga kasashen biyu, ba tare da wani bata lokaci a kan iyakokinsu ba.

Cinikayyar kayayyaki tsakanin Iran da Pakistan ta kai ta kimanin kudi dalar Amurka biliyan daya da miliyan 324 a kowace shekara, wanda kuma fara aiki da wannan sabon tsari zai habbaka cinikayyar fiye da sauran lokutan da suka gabata.

Tags

Ra'ayi