Jul 12, 2018 11:47 UTC
  • Wilayati Ya Gana Da Shugaban Rasha

Mai bawa jagoran juyin musulinci shawara kan harakokin siyasar kasa da kasa ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a yau Alhamis.

A yayin ganawar ta su, Ali Akbar Vilayati ya mekawa Shugaban kasar ta Rasha, sakon jogora juyin musulinci Ayatollahi Sayyid Ali Khamenei da na Shugaban kasar Dakta Hasan Rauhani.

A jiya Laraba ce mai bawa jagoran juyin musulincin na Iran Dr Ali Akbar Wilayati tare da rakiyar wasu manyan jami'ai na kasar suka isa birnin Moscow domin isar da sakon jagoran juyin musulinci da na Shugaba Rohani ga Shugaba Viladimir Putin na kasar Rasha.

Yayin da yake ishara kan alakar dake tsakanin kasashen biyu, Dakta Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa a shekarun baya bayan nan kasashen biyu sun kara daga alakar dake tsakanin su a yankin da kuma kasa da kasa.

Tags

Ra'ayi