• Iran Tana Goyon Bayan Kiran Tsagaita Wutar Yaki A Kasar Yemen

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ce; Kasar tana goyon bayan kiran da wasu fitattaun masana musulmi su ka yi na a kawo karshen yakin kasar Yemen

Bahram Kasimi ya jaddada cewa; Tun farkon yakin ne Jamhuriyar musulunci ta Iran take yin kira da a kawo karshensa, kuma ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya kaddamar da wani shiri da zai kai ga dakatar da yakin

Har ila yau, Bahram kasimi ya ce; Duk wani yunkuri da zai kai ga kawo karshen yakin kasar Yemen to jamhuriyar musulunci ta Iran tana goyon bayansa.

Wasu fitattun masana musulmi da su ka gabatar da taron karawa juna sani a kasar Jordan sun yi kira da a kawo karshen yakin Yemen da kuma bude tattaunawa a tsakanin banagarorin da suke da sabani da juna a karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya.

Saudiyya bisa goyon bayan Amurka ce take jagorantar yaki akan kasar Yemen wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane masu yawan gaske, tare da lalata cibiyoyin masu amfani ga al'ummar kasar.

Tags

Jul 18, 2018 06:59 UTC
Ra'ayi