Jul 25, 2018 19:31 UTC
  • Dr Ruhani: Hadin Kai Da Tsayin Dakar Al'ummar Iran Sune Manyan Martani Kan Barazanar Amurka

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Barazana da zarge-zarge marassa tushe da wasu jami'an Amurka suke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba su bukatar maida martani.

A jawabinsa a zaman taron majalisar ministocin kasar Iran a yau Laraba: Shugaban kasar Dr Hasan Ruhani ya jaddada cewa: Hadin kan al'ummar Iran da rashin damuwarsu da irin barazana da maganganu marassa tushe da wasu jami'an Amurka suke yi kan Iran, suna daga cikin manyan matakan maida martani kan kasar ta Amurka.

Har ila yau Dr Ruhani ya bukaci al'ummar Iran da su kara zage dantse a fagen rusa dukkanin makirce-makircen da makiya suke kitsawa kan kasarsu. Yana mai fayyace dalilin Iran na kai karar kasar Amurka gaban kotun duniya ta ICC da cewa: Mafi yawan kasashen duniya sun yi Allah wadai da matakan rashin adalci da kasar Amurka take dauka kan Iran, kamar yadda wasu kasashen suka bayyana rashin jin dadinsu da rashin adalcin na Amurka kan kasar ta Iran.

Tags

Ra'ayi