Aug 08, 2018 18:48 UTC
  • Shugaban Majalisar Dokokin Iran Ya Ce: Iran Zata Maida Martani Kan Bakar Siyasar Amurka

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran ya ce: Bakar siyasar kasar Amurka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata fuskanci maida martani mai gauni.

A ganawarsa da jakadan kasar Norway a kasar Iran Lars Nordrum a jiya Talata: Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Dr Ali Larijani ya tabo irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen yammacinTurai musamman ganawar da ta gudana a tsakaninsu bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar da duniya ta cimma da kasar ta Iran. Yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata ci gaba da gudanar da kyakkaywar alakar da ke tsakaninta da kasashen yammacin Turai.

Dr Larijani ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana cikin yaki ne da bakar siyasar Amurka, don haka Iran zata yi nazari kan irin martanin da ya dace ta mayar kan gwamnatin Amurka musamman shugaban kasarta Donald Trump.

Jakadar kasar Norway a Iran  Lars Nordrum ya jaddada cewa: Alakar da ke tsakanin kasashen Iran da Norway a harkokin Majalisa yana da kyau, kuma akwai bukatar bunkasa alakar da ke tsakaninsu a harkar tattalin arziki musamman a fagen kasuwanci.

Tags

Ra'ayi