• Mahajjata Aikin Hajjin Bana Sun Gudanar Da Tsayiwar Arafah A Filin Arafah A Yau

Mahajjata aikin hajjin bana sun gudanar da tsayiwar arafah a filin arafah na kasar Saudiyya a yau Litinin a matsayin rukunin farko na aikin hajji.

A yau Litinin 9 ga watan Zul-Hajj a bisa kidayar kwanakin watan Zul-Hajji a kasar Saudiyya; Mahajjata aikin hajjin bana da suka zo daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da rukunin farko na aikin hajji ta hanyar gudanar da tsayiwar Arafah a babban filin arafah, inda tawagar kasar Iran ta gudanar da addu'ar ranar arfah da aka ruwaito daga Imam Husaini jikan manzon Allah kuma daya daga cikin shugabannin samarin gidan aljanna {a.s} gami da karanta sakon jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ga mahajjatan bana.

A bayan faduwar rana a yau mahajjatan sun kama hanyar tafiya Mash'arul-Haram domin kwana a can, sannan a gobe Talata 10 ga watan zul-Hajj wato ranar babbar sallah bayan fitowar rana zasu kama hanyar tafiya Minna domin gudanar da ayyukan ranar lahiya da suka hada da jifa, yanka da sauransu.

Aug 20, 2018 18:14 UTC
Ra'ayi