Aug 31, 2018 18:54 UTC
  • IAEA: Iran Tana Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

A karo na goma 12 Hukumar makamashin Nukiliya ta Duniya ta fitar da rahoto da yake tabbatar da cewa Iran tana aiki da yarjejeniyar

Jakadan Iran a hukumar makamashin Nukiliya ( IAEA) Kazim Garib Abadi ya bayyana cewa; Wannan shi ne karo na 12 da hukumar take bayyana yadda Iran take aiki da yarjejeniyar.

Garib Abadi ya kuma ambato hukumar tana cewa; Tun daga ranar farko ta cimma yarjejeniyar hukumar makamashi ta kasa da kasa take sanya idanu akan ayyukan Iran, kuma  ko sau daya ba ta ga inda aka karya yarjejeniyar ba.

Hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ta fitar da wannan rahoton ne dai bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar a cikin watan Mayu.

Rahoto na 11 da hukumar ta fitar a ranar 6 ga watan Yuli na 2018 shi ma ya tabbatar da cewa Iran tana aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya.

Tags

Ra'ayi