Sep 02, 2018 06:43 UTC
  • Amurka Ta Sha Alwashin Tabbatar Da Kai Kawon Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Duk Tare Da Barazanar Iran

Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan cewa zata tabbatar da kai kawon jiragen kasuwanci a tekun farisa a duk lokacinda kasar Iran ta yi kokarin hana hakan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta nakalto hukumar "The Us Central Command (CENTCOM) tana fadar cewa zata tabbatar zirga zirgan jiragen kasuwanci a tekun farisa duk tare da barazanan da kasar Iran ta yi na dakatar da zirga zirgan jiragen idan an hanata saida danyen man fetur na kasarta.

Labarin ya kara da cewa CENTCON ta bayyana haka ne a jaridar Khaleej Times Daily ta kasar hadaddiyar daular larabawa a jiya Asabar. Jaridar ta nakalto wani jami'in CENTCOM Major Josh Jacques yana cewa Amurka ta kulla yerjejeniya da kasashe da dama na tabbatar da tsaro a  yankin, ba tare da ya bayyana sunan yankin da kasashen ba.

A cikin watan Nuwamba mai zuwa ne Amurka ta sha alwashin hana kasar Iran sayar da danyen man fetur na kasar kwata-kwata har sai da amince da tattaunawa ko kuma gwamnatin kasar ta fadi. 

 

Tags

Ra'ayi