Sep 05, 2018 19:07 UTC
  • Kasar Iran Ta Jaddada Batun Yaki Da Masu Kirkiro Kungiyoyin 'Yan Ta'adda

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren dokoki da harkokin kasa da kasa ya jaddada daukan matakan da suka dace wajen kawo karshen akidar wuce gona da iri da ke haifar da ayyukan ta'addanci a duniya.

A jawabinsa a zaman taron kasa da kasa kan yaki da fataucin muggan makamai da kuma ta'addanci a birnin Moscow na kasar Rasha: Gholam Husaini Dehqani ya bayyana cewa: Ayyukan ta'addanci da wuce gona da iri kan al'umma suna ci gaba da wanzuwa ne sakamakon yadda masu goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya suke aike musu da makuden kudade da makamai a sassa daban daban na duniya.

Husaini Dehqani ya kara da cewa: Ganin yadda ta'addanci ya zame babbar barazana ga duniya, dole ne kasashen duniya su hada hannu wajen yakarsa da nufin murkushe shi baki daya.

Dehqani ya jaddada yin gargadi kan yadda kungiyoyin 'yan ta'adda suke suke amfani da hanyoyin sadarwa ta zamani wajen yada munanan akidunsu tare da kulla yarjejeniyar mallakar makamai. 

Tags

Ra'ayi