Sep 07, 2018 05:44 UTC
  • A Yau Juma'a Za A Yi Taro Tsakanin Shugabannin Kasashen Iran, Trukiya Da Rasha A Tehran

Wani jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Iran Sadiq Husain Jabiri Ansari ya ce; Tuni an kammala tsara bayanin bayan taron na bangarori uku a Tehran

Jabir Ansari ya ci gaba da cewa; Za a yi taron na Tehran ne adaidai lokacin da wani sashe na kasar Syria yake ci gaba da zama a karkashin 'yan ta'adda.

Jabir Ansari ya kuma ce; Yankin Idlib ne kadai wurin da ya rage a kasar Syria da yake a karkashin 'yan ta'adda.Har ila yau, jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce dukkanin kasashen uku da suke taro a Tehran suna fuskatar takunkumi daga kasar Amurka.

Kwararru daga kasashen uku sun yi zama na musamman anan Tehran inda su ka fitar da bayanin da zai zama na bayan taron shugabannin kasashen.

 

Tags

Ra'ayi