Sep 08, 2018 06:47 UTC
  • Iran Ta yi Allawadai da Kona Karamin Ofishin Jakadancinta A Basra Na Kasar Iraqi

Gwamnatin kasar Iran ta yi Allawadai da kona karamin ofishin jakadancinta da ke birnin Basra na kudancin kasar Iraqi

Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta nakalto Bahram Qassemi kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran yana fadar haka a jiya Jumma'a ya kuma kara da cewa masu zanga zangar sun kona ofishin jakadancin kumus amma babu wani jami'in diblomasiyyar kasar da abin ya shafa. 

Banda haka Qassemi ya bukaci gwamnatin kasar Iraqi ta kama wadanda suka yi wannan aika aikan ta hukuntasu sannan tun farko alhakinta ne ta hana hakan aukuwa a matsayinta na mai kare lafiya da dukiyoyin jami'an diblomasiyyar kasashen waje. 

Banda haka kakakin ma'aikatar harkokin wajen ya ce ma'aikatar ta kira jakadan kasar Iraqi a nan Tehran a jiya jumma'a don bayyana masa damuwarta kan abinda ya faru a basara. 

Kafin haka dai masu zanga zangar neman kyautata rayuwa a birnin sun kona ofisodhin gwamnati da dama a cikin watannin da suka gabata.

 

Tags

Ra'ayi