Sep 09, 2018 07:30 UTC
  • Ministan Tsaron Iran: Amurka Tana Amfani Da 'Yan Ta'adda Don Cimma Muradinta

Ministan tsaron kasar Iran, Birgediya Janar Amir Hatami, ya bayyana cewar Amurka tana amfani da duk wata dama da take da ita ciki kuwa har da amfani da kungiyoyin 'yan ta'adda don cimma manufa da muradinta ba tare da la'akari da muradin sauran kasashen duniya ba.

Birgediya Janar Amir Hatami, ministan tsaron na Iran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da mataimakin shugaban babbar cibiyar tsaro ta kasar China Janar Zhang Youxia a birnin Beijing, babban birnin kasar Chinan a jiya Asabar inda ya ce karen tsayen da Amurka take yi wa dokoki da kuma yarjejeniyoyi na kasa da kasa ciki kuwa har da yarjejeniyar nukiliyan Iran da yarjejeniyar dumamar yanayi na Paris suna daga cikin matakan da Amurkan take dauka da ke barazana ga zaman lafiyan duniya.

Har ila yau kuma ministan tsaron na Iran yayi ishara da irin rawar da Iran da Rasha da kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon suke takawa wajen fada da ta'addanci a kasar Siriya yana mai jinjinawa irin rawar da China ma take takawa a wannan fagen.

A yayin ganawar dai bangarori biyu sun tattaunawa hanyoyin da kasashen biyu za su bi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin Gabas ta tsakiya da ma duniya baki, kamar yadda kuma suka jaddada wajibcin aiwatar da yarjejeniyoyin tsaro da kasashen biyu suka cimma da nufin fada da ta'addanci.

 

Tags

Ra'ayi