Sep 09, 2018 19:08 UTC
  • Babban Kwamandan Sojojin Iran: Al'ummar Kasar Ta Tilastawa Amurka Ja Baya

Babban kwamandan Sojojin kasar Iran ya tabbatar da cewa juriyar da jamhoriyar musulinci da al'ummar kasar Iran suka yi a gaban Amurka ya tabbatar da cewa idan al'umma ba ta ji tsoron masu takama da karfi ba, ta kuma yi dogaro da karfinta, za ta tilastawa masu ji da karfin Duniya ja da baya

A yayin da ya halarci bikin yaye daliban sojojin ruwa na kasar da ya gudana a safiyar wannan lahadi, Jagoran juyin juya halin musulunci  Sayyid Aliyul-Khaminai, babban kwamandan sojojin kasar Iran ya yi ishara kan mumunar siyasar masu girman kai na samar da rashin tsaro a yankin inda ya ce masu girman kai na Duniya, musaman ma kasar Amurka suna  kare manufofinsu ta hanyar samar da yakin cikin gida, fadada ayyukan ta'addancin a yankin, kuma abin bakin ciki wasu kasashen yankin na taimaka musu  wajen cimma mumunar wannan manufa.

Babban kwamandan Sojojin kasar Iran din ya bayyana shirin Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila na hana wanzuwa da kuma fadadar  karfin musulinci a yankin, inda ya kara da cewa masu girman kai na Duniya sun san cewa sakon musulinci shi ne bayar da kariya ga masu karamin karfi da talakawa gami da mabukata na Duniya don haka suke kokarin dakile duk wani karfi na musulinci.

Jagoran juyin juya halin musulunci  Sayyid Aliyul-Khaminai ya ce juriya da kuma tsayin daka da jamhoriyar musulinci ta Iran ta yi a gaban masu girman kai na Duniya ya tilasta musu ja da baya da kuma rusa duk wasu manufofinsu na zalinci a Duniya, inda ya kara da cewa masu sharhi na Duniya na cewa dogoron da jamhiroyar musulinci tayi da Allah da kuma karfin al'ummar kasarta ya sanya masu girman na Duniya ja da baya.

Tags

Ra'ayi