Sep 12, 2018 07:26 UTC
  • Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Hadin Kan Al'ummar Musulmi

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran ya jaddada wajabcin hadin kan al'ummar musulmi musamman ganin yadda makiya addinin Musulunci suke ci gaba da kokarin raba kan al'ummar musulmi ta hanyoyi daban daban.

A ganawarsa da manyan malaman ahlus-Sunna da na Shi'a a ziyarar da ya kai zuwa karamar hukumar Larestan da ke lardin Fars a shiyar kudancin kasar Iran a jiya Talata: Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa: A irin halin da ake ciki yanzu ganin yadda makiya suka yunkuro da dukkanin karfinsu domin ganin sun rusa addinin Musulunci tare da wurga al'ummar musulmi cikin rikici da juna, dole ne al'ummar musulmi su fadaka tare da shiga cikin taitayinsu ta hanyar hada kansu tare da yin watsi da dukkanin bambance-bambancen da ke tsakaninsu na mazhaba.

Har ila yau Dr Larijani ya kara da cewa: Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kama hanyar rikita harkokin kasa da kasa da nufin janyo rudani a duniya musamman matakin da ya dauka na ficewa daga yarjejeniyar kasa da kasa da aka cimma da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan shirinta na nukiliya, amma a halin yanzu haka shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun bukaci mahukuntan Iran da kada su hanzarta maida martani domin zasu ci gaba da daukan matakan da suka dace wajen ganin yarjejeniyar ta ci gaba da gudana kamar yadda aka cimma. 

Tags

Ra'ayi