Sep 19, 2018 05:36 UTC
  • Qassemi: Babu Gaskiya Cikin Zargin Da Ministan Harkokin Wajen Moroko Yayi Kan Iran

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da kalaman da ministan harkokin wajen kasar Moroko Nasser Bourita yayi kanta, tana mai bayyana kalaman nasa a matsayin wasu maganganu marasa tushe da makama.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Kasar Iran din Bahram Qassemi ne ya bayyana hakan inda yace abin da ministan harkokin wajen na Moroko ya fadi maimaici ne na maganganun da masu kokarin haifar da rikici da rarrabuwan kai tsakanin musulmi suke yi.

Ministan harkokin wajen kasar Morokon, Nasser Bourita, a wata hira da yayi da kafar watsa labaran Breitbart News Network ta kasar Amurka ya zargin Iran da aikata ayyukan masu cutarwa a yankin Arewacin Afirka yana mai cewa kasar Moroko tana goyon bayan matakan da shugaban Amurka  Donald Trump yake dauka kan Iran.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran dai yayi watsi da wadannan kalaman yana mai cewa: Alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran  da kasashen Afirka wata alaka ce ta girmama juna da kuma kiyaye hurumin dukkanin bangarori. Qassemi ya kara da cewa kamata yayi kasar Moroko ta ba da himma wajen kare muradunsa da na al'ummarta maimakon ta mai da kanta  'yar amshin shantan manyan kasashen duniya.

Kasar Moroko dai ta kashe alakarta ta diplomasiyya da Iran a shekara ta 2009 kana daga baya kuma ta dawo da ita a shekara ta 2016, sannan kuma ta sake katse ta a ranar 1, Mayun 2018 wanda ake ganin ta yi hakan ne don dadada wa wasu kasashen musamman Saudiyya.

 

Tags

Ra'ayi