Sep 21, 2018 17:59 UTC
  • Qassemi: Iran Ba Ta Da Bukatar Wata Ganawa Da Trump

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya karyata rahotannin da ke cewa Iran ta bukaci ganawa da Trump.

A cikin wani bayani da ya fitar a yammcin yau Juma'a, Bahram Qasemi ya bayyana cewa babu gaskiya dangane da wasu rahotanni da wasu kafofin yada labarai na Amurka suka bayar, da ke cewa jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya Nikki Haley ta bayyana cewa Iran ta bukaci ganawar shugabanta da Donald Trump a gefen babban taron majalisar dinkin duniya.

Qasemi ya ce idan da haka ne da babu wani abin da zai buya ga duniya, kuma tun kafin wannan lokacin Amurka ta sha nemen a gudanar da irin wannan ganawa amma Iran tana kin amincewa.

Ya ce Iran ba ta da bukatar ganawa da Trump, domin kuwa Amurka ta tabbatar wa duniya matsayinta na rashin alkawali, akan babu wani abin da za a tattaunawa  a kansa tsakaninta da Iran.

 

Ra'ayi