Sep 22, 2018 06:26 UTC
  • An Fara Bikin Makon Tsaron Kasar A Iran

A yau Asabar ne 22 ga watan Satumba ake tunawa da yakin da Iraki ta kallafawa Iran, wanda ake kira da makon tsaron kasa mai tsarki

A cikin watan Satumba na 1980 ne Sadam ya shelanta yaki akan Iran da zummar cewa a cikin mako guda zai kwace iko da Tehran.

A ranar 31 ga watan Shahribar wanda shi ne wata na shida a kalandar hijira shamshiyya, ake fara bukukuwan makon tsaron kasa a nan Iran. A cikin wadannan kwanakin na mako ana gabatar da bukukuwa daban-daban a dukkanin fadin kasar.

Gwamnatin Saddam ta Ba'asiyya ta sami dukkanin taimako da tallafi daga manyan kasashen duniya domin yakar jamhuriyar musulunci ta Iran, wanda ya dauki tsawon shekaru 8 ana yi.

Sai dai al'ummar Iran bisa dogaro da Allah ta yi tsayin daka da jajurcewa da kin mika kai ga masu girman kai da su ka ingiza Saddam domin yakar jamhuriyar musulunci ta Iran.

Ra'ayi