Sep 22, 2018 06:33 UTC
  • A cikin Watanni 6 Iran Ta Sayar Da Habar Da Ba Ta Man fetur Ba Ta Dala Biliyan 19

Shugaban babban Bankin Jamhuriyar musulunci ta IRan ne ya bayyana cewa a cikin watanni shida na farkon wannan shekara ta hijira shamshiyya Iran ta fitar da hajar da kudinta ya haura dala biliyan 19

Abdunnasir Himmati ya kara da cewa tuni dala biliyan 3 da aka sayar da iskar Gas da dangogin man fetur an sake mayar da su cikin harkokin kasuwanci da tattalin arziki, yayin da saura dala biliyan 16 za su biyo baya.

Shi ma shugaban kungiyar ci gaban kasuwanci ta Iran Mujtaba Khusrotaj ya bayyana cewa; An sami karuwar fitar da hajar da ba man fetur ba wacce ta kai kaso 14% a cikin watanni 4.

Khusrotaj ya kara da cewa Idan aka kwatanta hajar da aka sayar ta fuskar masan'antu da ma'adanai na shekarar bana da kuma na shekarar bara, to an sami karin kaso 16%, wanda ya kama akan dala biliyan 9.8.

Ra'ayi