• Duniya Na Ci Gaba Da Allawadai Da Harin Ahwaz A Iran

Kasashen na duniya na ci gaba da aikewa da sakon ta'aziya ga al'ummar Iran, bayan harin ta'addancin da ya yi sanadin shahadar mutane akalla 29 a garin Ahwaz dake Kudu maso yammacin Iran a yau Asabar.

Shugaba Rasha Fladimir Putin shi ne wani shugaban kasa na farko da mika ta'aziyarsa ga Iran, tare da yin allawadai da harin, a yayin wata zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Iran, Hassan Ruhani.

Mista Putin ya kuma ce kasarsa a shirye take koda yaushe domin kara hadin gwuiwarta da Iran ta yadda zasu kara yakar ta'addanci.

Ko baya Rasha, kasashen da suka hada da Pakistan, Turkiyya, Iraki, Siriya, Armenia, Da Spain ta hanyar ma'aikatocin harkokin wajensu sun yi allawadai da harin.

Shi mai jakadan Biritaniya a nan birnin Tehran, ya wallafa a shafinsa na Twetter cewa yana mai allawadai da harin.

Hukumonin Tehren dai na zargin kungiyar 'yan ta'adda ta al-Ahwaziya dake samun goyan bayan Saudiyya da kai harin, a yayinda kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta fitar da sanarwar cewa ita ce keda alhakin kai harin. 

Tags

Sep 22, 2018 17:17 UTC
Ra'ayi