Sep 23, 2018 11:48 UTC
  • Shugaban Kasar Iran Ya Kama Hanyar New York Don Halartar Taron MDD

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya kama hanyar birnin NewYork na kasar Amurka don halarttar taron shekara shekara na majalisar dinkin duniya karo na 73.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa tare da shugaban kasar akwai ministan harkokin wajen kasar Mohammad Jawad Zarif, Mataimakin ministan harkokin Abbas Araqchi da kuma wasu manya manyan jami'an gwamnatin kasar. 

Ana saran shugaban Ruhani zai yi jawabi a gaban babban zauren majalisar, sannan zai halarci tarin girmama tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela wanda hukumar kare hakkin bil'adama na majalisar ta shirya. 

Banda haka shugaban Ruhani zai gana da wasu shuwagabannin kasashen duniya wadanda suka halarci taron da kuma kafafen yada labarai na duniya har'ila yau da kuma Iraniyawa mazauna Amurka da kuma shuwagabannin wasu kasashe da kungiyoyin addinin  musulunci.

Tags

Ra'ayi