Sep 23, 2018 17:43 UTC
  • Dakarun Kare Juyi Da Ma'aikatar Tsaron Cikin Gidan Iran Sun Sha Alwashin Daukar Fansar Harin Ahwaz

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) da Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na Iran sun sha alwashin daukar fansa a kan 'yan ta'addan da suka kai harin garin Ahwaz da yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunana wani adadi na al'ummar kasar ta Iran.

A wata  sanarwa da suka fitar a yau din nan Lahadi, Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musuluncin sun ja kunnen 'yan ta'addan da cewa nan ba da jimawa ba za su fuskanci gagarumin mayar da martani a matsayin daukar fansar jinin shahidan da suka zubar.

Dakarun na IRGC sun kara da cewa: Harin ta'addancin da 'yan amshin shatan ma'abota girman kan duniya da kuma kasashen da aka bar su a baya suka kai garin na Ahwaz wata alama ce da take nuni da cewa makiyan al'ummar Iran da suka hada da babbar shaidaniyya (Amurka), Sahyoniyawa da kuma wasu kasashen larabawa, a shirye suke su yi amfani da dukkanin karfinsu wajen cutar da al'ummar Iran ciki kuwa har da zubar da jinin mata da kananan yara, don haka suka ja kunnen su da cewa su zauna cikin shirin fuskantar kakkausar mayar da martani daga wajensu.

Ita ma a nata bangaren, Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri ta Iran ta bakin ministan ma'aikatar Sayyid Mahmud Alawi ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani mai kaushi ga wadanda suka shirya da kuma aiwatar da wannan hari na ta'addanci.

Sayyid Alawi ya kara da cewa jami'an tsaron Iran sun kuduri aniyar bin sahun wadannan 'yan ta'addan sannan kuma ba za su taba hutawa ba har sai sun dau fansa a kan wadannan 'yan ta'addan.

A jiya ne dai wasu 'yan ta'adda da jami'an Iran din suka ce suna samu daurin gindin bayan wasu kasashen waje suka kai hari a wajen faretin soji da ake gudanarwa a garin Ahwaz lamarin da yayi sanadiyyar shahadar sama da mutane 25 da kuma raunana wasu da daman gaske.

Tags

Ra'ayi