Oct 20, 2018 18:21 UTC
  • Iran Ta Bukaci Pakistan Da Ta Dau Matakan Gaggawa Wajen Sako Jami'an Tsaron Iran Da Aka Sace

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bukaci gwamnatin kasar Pakistan da ta gaggauta daukan matakan da suka dace wajen ganin an sako wasu jami'an tsaron kan iyakan kasar Iran da 'yan ta'adda suka sace a lardin Sistan wa Baluchestan da ke kan iyaka da kasar Pakistan din.

Janar Baqeri ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da hafsan hafsoshin sojin kasa na kasar Pakistan Janar Qamar Javed Bajwa inda ya bayyana masa cewa bisa ga yarjejeniyar da sojojin kasashen biyu suka sanya wa hannu kan tabbatar da tsaron kan iyakokin kasashen biyu, don haka muna fatan sojojin Pakistan za su dau matakan gaggawa wajen ganin an sako sojojin Iran da masu gadin kan iyakan kasar da aka sace.

Shi ma a nasa bangaren, Janar Bajwa ya bayyana damuwarsa da kuma ta gwamnatin Pakistan dangane da abin da ya faru din yana mai bayyana wa jami'in na Iran kokarin da gwamnatin Pakistan din take yi wajen kwato wadannan sojoji na Iran.

A kwanakin baya ne dai wasu 'yan ta'adda da suke samun goyon bayan wasu kasashen waje suka kai hari wani sansanin jami'an tsaron kan iyaka na Iran inda suka yi awun gaba da wasu sojojin da 'yan sanda masu gadin kan iyakokin su 14. Kungiyar nan dake kiran kanta Jaish ul-Adl da ke zaune a kasar Pakistan din ta sanar da cewa ita ce ta sace jami'an tsaron.

 

Tags

Ra'ayi