Nov 14, 2018 11:56 UTC
  • An Kame Wani Gungun Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Na Kasa Da Kasa A Iran

Jami'an tsaron kasar Iran sun samu nasarar tarwatsa wani gungun masu safarar miyagun kwayoyi tare da kama sama da ton 6 na kwayoyi a jahar Azarbajan ta yamma dake yamma maso arewacin kasar

A yayin kai farmakin, jami'an tsaron kasar ta Iran sun cabke mutum 11 dukkanin 'yan kasashen Turai tare kuma da miyagun kwayoyi sama da ton 6.

A shekarun baya-bayan nan, jami'an tsaron jamhoriyar musulinci ta Iran sun samu nasarar cabke gungun masu safarar miyagun kwayoyi da dama wadanda suke shigo da miyagun kwayoyi daga kasashen Turai zuwa jamhoriyar musulinci ta Iran din domin ruguza tarbiyar matasan kasar.

Sama da shahidai dubu uku da 800, jamhoriyar musulincin ta Iran ta bayar a yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a yankin.

Dangane da wannan batu, Majalisar Dinkin Duniya ta bata tuta na kasashen dake yaki da safarar miyagun kwayoyi.

Tags

Ra'ayi