Nov 16, 2018 19:07 UTC
  • Limamin Juma'a: Donal Trump Ya Kara Bakanta Sunan Amurka A Duniya

Limamin da ya jgorancin sallar juma'ar birnin tehran ya bayyana cewa Shugaba Donal Trump ya kara bakanta sunan Amurka a Duniya

Ayatollahi Muhamad Imami Kashani Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na nan birnin Tehran ya bayyana cewa duk da irin wanzar da fasadi da kuma zubar da jini gami da goyon bayan ta'addancin haramtacciyar kasar Isra'ila da mahukuntar Ali-sa'oud wajen zubar da jinin musulimi a Duniya to amma a tarihin shugabanin kasar Amurka babu wani shugaba ya bakanta kasar kamar Donal Trump. 

Ayatollahi Muhamad Imami Kashani ya ce a halin da ake ciki kasashen Duniya na baya-baya da kasar Amurka, wanda kuma hakan ke nuna cewa a ko wata rana kasar na kara yankwan jini  a Duniya.

Yayin dake ishara kan matsayin kasar Iran a idan al'ummar Duniya, Limamin ya ce a ko wata rana mutunci da karamcin tsarin musulinci na jamhoriyar musulinci ta Iran na karuwa a idanun al'ummar Duniya sabanin farfagandar karya da Amurka ke yi kan kasar ta Iran, hakika tsarin musulinci, tsari ne na zaman lafiya ba na zubar da jini ba.

Yayin da ya koma kan irin ta'adancin da sahayuna ke yi kan al'ummar Palastinu da kuma ta'adancin Saudiya kan Al'ummar Yemen, Ayatollahi Muhamad Imami Kashani ya ce dukkanin wannan ta'addanci na gudana ne bisa goyon bayan Amurka.

 

Tags

Ra'ayi