Dec 09, 2018 06:47 UTC
  • Jamus Da Faransa Za Su Samar Da Hanyar Mu'amalar Kudade Tare Da Iran

Rahotanni daga kasar Jamus na cewa, gwamnatocin kasashen kasar ta Jamus da kuma Faransa, sun cimma matsaya kan samar da hanyar ta'ammuli da kudade tare da kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, kasashen na Jamus da Faransa suna da nufin aiwatar da wannan shiri ne domin tabbatar da cewa sun kare dukkanin harkokin kasuwanci tsakanin Iran da kasashen turai, ta yadda takunkumin Amurka ba zai hana gudanar da mu'amalar kasuwanci a tsakaninsu ba.

Rahoton ya ce tsarin na SPV zai shafi hada-hadar kudade ne ba tare da hakan ya shafi bankunan kasar Amurka ba, kuma wani bajamushe ne zai jagoranci shirin daga kasar Faransa, inda a halin yanzu kasashe 9 daga cikin kungiyar tarayyar turai sun bayyana cewa a shirye suke su shiga cikin shirin, daga cikinsu kuwa har da Italiya, Spain, Austria, Belgium, Luxumburg da kuma Holland.

Wannan mataki dai na zuwa ne domin kare kyakkyawar alaka ta kasuwanci da tattalin arziki da ke tsakanin kasashen kungiyar tarayyar turai da kuma kasar Iran, daga takunkumin da Amurka ta sake kakaba wa Iran, bayan ficewarta daga yarjejeniyar nukiliya da ka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen kasashen duniya.

Ra'ayi