Dec 09, 2018 15:25 UTC
  • Iran : An Cafke Mutum 10 Bayan Harin Chabahar

'Yan sanda a Iran, sun cafke mutum 10, a ci gaba da binciken da ake bayan harin ta'addancin da ya janyo shahadar 'yan sanda biyu a yankin kudu maso gabashin kasar a ranar Alhamis data gabata.

'Yan ta'adda Ansar al-Furqan, ne dai suka dauki alhakin kai kan wani ofsihin 'yan sandan na Chabahar, dake yankin Sistan-Baloutchistan, saidai hukumomin sun yi watsi da ikirarin kungiyar.

Bayan harin dai ministan harkokin wajen kasar, Mohammad Javad Zarif, ya ce 'yan ta'adda dake samun dauki ne daga kasashen ne suka kai harin.

Jamhuriya Musulinci ta Iran dai na zargin kasashen Amurka, da Isra'ila da kuma Saudiyya da goya ma wadannan kungiyoyin baya.

A safiyar Alhamis data gabata ne wani dan kunar bakin wake cikin mota ya yi kokarin aukawa ofishin 'yan sanda na Chabahar, saidia yunkurinsa ya cutura motar ta tarwatse tun kafin ya kai ga ofishin, lamarin da ya yi sanadin shahadar 'yan sanda biyu da raunata wasu mutane da dama.

 

Tags

Ra'ayi