Dec 12, 2018 19:18 UTC
  • Jagora: Amurka Tana Tallafawa Saudiya A Ta'asar Da Take Aikatawa A Yemen

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Khaminae ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amarka tana taimakawa gwamnatin kasar Saudia a ta'asar da take aikatawa a kasar Yemen.

Jagoran ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da iyalan shahidai a gidansa a yau laraba, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana taimakawa kasar Saudia a yakin da ta fara a kasar Yemen tun shekara ta 2015, yakin da take tsammanin zata kammalashi a cikin yan makonni ko watanni idan yayi yawa. 

A wani wuri a jawabinsa jagoran ya ce gwamnatin kasar Saudia tana hada kai da makiya addinin musulunci wajen cutar da musulmi.

Dangane da takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar Iran kuma jagoran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana kara karfi duk tare da matsin lamban da Amurka takewa kasar, kuma Amurka bata yi wani abu a bayaba kuma nan gaba ma da yardar Allah ba zata iya yin kome ba. 

Jagoran ya yi watsi da fatan da gwamnatin Amurka take yi na cewa gwamnatin JMI ba zata ga bakin cika shekaru 40 da samuwar JMI ba. wato a shekara ta 2019.

Daga karshe jagoran ya bayyana sunan da Imam Khomanini (r) wanda ya kafa JMI ya bawa Amurka na cewa ita ce babbar Shaitan, ya farkar da mutanen duniya hakikanin yadda gwamnatin Amurka take.

 

Tags

Ra'ayi