Dec 13, 2018 19:02 UTC
  • Tarayyar Turai Na Kokarin Ganin Tsarin Musayar Kudade Da Iran Ya Fara Aiki

Tarayyar Turai ta bayyana cewa tana aiki dare da rana don ganin sabon tsarin musayar kudade da harkokin kasuwanci tsakanin ta da Iran ya fara aiki.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tsohuwar shugaban majalisar dokokin tarayyar Turai kuma shugaban tawagar karfafa dangantaka da Iran Tarja Cronberg tana fadar haka a yau Alhamis a nan Tehran.

Labarin ya kara da cewa shirin wanda ake kira "Special Vehicle Purpose" ko (SPV), wani tsarin musayar harkokin kasuwanci ne da kasar Iran don karya takunkuman da gwamnatin kasar Amurka ta dorawa JMI.

Tarja Cronberg ta kara da cewa tsarin zai fara aiki kafin karshen wannan shekara, sannan kananan kamfanoni da matsakaita ne zasu fi amfana da tsarin, ta ce tsarin yana bukatar horaswa tsakanin yan kasuwa da zasu amfana da shi a nan Iran da kuma kasashen na Turai.

A yau Alhamis ne Tarja Cronberg ta gana da shugaban cibiyar kasuwanci na kasar Iran Gholam-Hossein Shafei, inda ta fada masa cewa tsarin idan ya kammala zai bada damar shigo da magunguna da abinci daga kasashen turai ba tare da wata matsalaba. 

A cikin takunkuman da gwamnatin Amurka ta sanyawa kasar Iran dai akwai na hana shigo da magani da kuma abinci, sannan ta yi barazanar hukunta duk wani kamfanin da ya sabawa takunkuman nata.

Kafanonin kasashen turai da dama suna jenya daga Iran don tsaron kada Amurka ta dora masu takunkuman sayar masu da dalar Amurka.

 

Tags

Ra'ayi