Jan 01, 2019 15:15 UTC
  • Gidan Talabijin Na Hausatv Ya Fara Watsa Shirye Shiryensa A Nau'in Hoto (HD)

Shugaban tashar talabijin din kasa da kasa ta Hausatv, Dr. Muhammad Reza Hatami ya sanar da fara watsa shirye-shiryen wannan tasha ta Hausatv da za a ci gaba da yi a awoyi 24 bisa yanayin hoto mai inganci nau'in (HD).

Ya bayyana cewa wannan tasha tana watsa shirye -shirye na sa'o'i shida a kowace rana, sannan kuma ta sake maimaita wa sau uku daidai da yanayin lokutan da ke nahiyar Afirka.

Kamar yadda sunanta ke nuna wa, Hausatv ta game kasashen Afirka ne masu magana da harshen Hausa, wadanda suka hada da, Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Chadi, Benin, Ivory Coast, Mali, Togo, Burkina Faso, Sudan, Afrika ta Tsakiya, Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, Congo da Saliyo. 

Har ila yau ya kuma kara da cewa, bisa yin la'akari da kasantuwar yaren gwamnatocin kusan kashi 82 daga cikin dari na kasashen masu magana da harshen Hausa ke rayuwa a ciki Turanci ne saboda haka Hausatv ke watsa shirye-shirye a bangare guda da Harshen Turancin Ingilishi.

Haka kuma bisa la'akari da cewa harshen gwamnati na kusan mutanen Afirka su miliyan 700, Turanci ne, Hausatv ke watsa shirye-shirye na awoyi 24 ta hanyar intanet kuma a kai tsaye cikin harsunan Hausa da Turanci wanda za a iya samunsu a wannan shafi namu na intanet kamar haka: ha.hausatv.com da kuma hausatv.com

Kashi 73 daga cikin dari na masu yin amfani da harshen Hausa suna zaune a kasar Najeriya, wadda kasa ce mai dauke da jama'a masu yin amfani da intanet da yawansu ya kai miliyan 183.

Bisa kididdigar da aka fitar a watan jiya Najeriya ce ta 8 a jerin sunayen kasashe masu yin amfani da intanet, kasar Iran kuwa ita ce ta 13 a kididdigar.

Dr. Hatami ya kuma kara da cewa " Zuba hannun jari na kasashen waje a shekarar 2018 ya karu har zuwa dala biliyan 200.

Afirka ta jawo hankalin kasashe wadanda suka hada da Amurka, Sin, Ingila, Jamus, Faransa, Indiya, Rasha da Japan, haka kuma a 'yan shekarun baya bayan nan, makobtanmu ma da suka hada da Saudiyya, Turkiyya, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), su ma sun bi sahun masu saka hannun jari a Afirka ta yadda suka kafa kafofin sadarwa a Afirka.

Shugaban na Hausatv har ila yau ya kara da cewa sanya karfin zuba jari a Afirka zai iya zama daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da za su iya rage matsalar takunkumin Amurka a kan Iran, ko da dai yanayin musayar cinikayya tsakanin Iran da kasashen Afirka, wato yawan shiga da fitar kayayyakin cinikikayya daga Iran zuwa Afirka bai ma kai na biliyan daya ba wanda ke nuni da cewa ba abin kwatanta wa ba ne da yawan cinikin da makwabtanmu keyi da Afirka.

Dr. Hatami yana da imanin cewa karkatar da hankalin jama'a da kuma sanya rudu da kafofin yada labarai na kasashen waje suka kasance suna yi  da kuma fassara hakan da kafofin cikin gida suke yi ya haifar da rashin fahimtar cikakkiyar sura ta Afirka a tunanin jama'a kuma wannan ne daya daga cikin abubuwan da suka kawo rashin samun hadin gwiwa tsakanin Iran da Afirka.

Daga karshe shugaban na Hausatv ya nuna kyakkyawan fatansa na cewa shirye-shiryen rediyo da talabijin na Hausatv za su iya fito da cikakkiyar sura ta Iran da Afirka, abin da zai iya samar da ci gaban hadin gwiwa domin yin aiki tare.

Tashar Hausatv wadda wani sashe ne na hukumar gidan Radiyo da Talabijin ta Iran, ta fara watsa shirye-shiryenta ne tun a watan Yuli na shekara 2018.

Tags

Ra'ayi