Jan 08, 2019 06:53 UTC
  • Babban Bankin Iran Ta Gabatar Da Bukatar A Cire Sifiri 4 Daga Kudaden Kasar

Ministan tattalin arziki da baitul mali na kasar Iran ya bayyana cewa batun shafe sifiri guda 4 a cikin kudaden Iran yana gaban kwararru don bada shawara kan aikin.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar ta Iran ya nakalto Farhad Daj-Pasanda yana fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa, ra'ayin kwararru a tattalin arziki shi ne zai fayyace yiyuwan aiwatar da shirin ko kuma barinsa. 

A ranar Lahadin da ta gabata ce shugaban babban bankin kasar ta Iran ya gabatarwa komitin tattalin arziki na majalisar dokokin kasar bukatar a shafe sifiri 4 a kudaden kasar don daga darajarsu. 

Abdunnasir Himmata wani masanin harkokin tattalin arziki a ma'aikatar ya bayyana cewa idan an amince da shirin shafe sifiri 4 a kudaden kasar, za'a aiwatar da shi a cikin shekaru biyu masu zuwa. 

Tags

Ra'ayi