Feb 17, 2019 11:03 UTC
  • Iran : Zarif, Ya Maida Kakkausan Martani Ga Mike Pence

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya yi tir da allawadai da kalamman da ya danganta dana kiyaya da marar tushe da mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence ya firta kan kasar ta Iran.

A cewar Mista Zarif, kalamman na Pence, marasa tushe ne da kuma kiran nuna kiyaya ga kasar ta Iran.

Martanin na Zarif, na zuwa ne kan kalamman da mataimakin Amurka ya firta sau biyu a jere a cikin makon nan a yayin tarukan Varsovie dana Munich, inda yake zargin kasar ta Iran da tana fitina a yankin da kuma neman mallakar makamman nukiliya.

Mista Zarif wanda ke halartar taron tsaro a birnin Munich, ya ce kiran da mataimakin shugaban Amurka ya yi ga kasashen turai a cikin nahiyar ta Turai kuma na neman su janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, zagon kasa ne ga harkokin tsaro kuma masu hadarin gaske.

Tags

Ra'ayi