Apr 21, 2016 10:47 UTC
  • An Fara Yakin Neman Zaben Zagaye Na Biyu Na Zaben Majalisar Dokokin Iran

A safiyar yau Alhamis ne aka bude kofar yakin neman zabe a zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran da za a gudanar a ranar 29 ga watan Aprilun nan da muke ciki.

Ma'aikatar cikin gidan Iran, wacce ita ce take da alhakin tsara zaben ta ce kimanin 'yan takara 136 ne za su yi takarar kujeru 68 da suka rage cikin kujeru 290 da majalisar ta ke da su bayan zagayen farko na zaben da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata.

Shugaban cibiyar zaben a ma'aikatar cikin gidan ta Iran Malam Muhammad Husain Moqimi ya ce an tanadi rumfunan zabe kimanin 15,350 a dukkanin larduna 21 da za a gudanar da zaben, kamar yadda ya ce za a gudanar a zabubbukan ne a garuruwa 55 a duk fadin kasar ta Iran.

Zaben 'yan majalisar shawarar Musuluncin ta kasar Iran da aka gudanar da zagayensa na farko a watan Fabrairun da ya gabata shi ne na farko da aka gudanar a kasar tun bayan yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya lamarin da ya janyo hankulan duniya sosai.

Tags

Ra'ayi