Mayu 07, 2016 18:19 UTC
  • Ministan Tsaron Iran Ya Ce Babu Wanda Ya Isa Ya Takaita Atisayen Sojin Kasar

Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Husain Dehqan ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba ta da wani kan iyaka dangane da atisayen da sojojinta suke yi a cikin ruwayen kasar da ke Tekun Fasha da kuma Tekun Oman

Janar Dehqan ya bayyana hakan ne a yau Asabar din inda ya ce Iran dai ba ta ganin akwai wani haddi ko kan iyaka da wani zai sa mata dangane da atisayen da sojojinta suke yi, yana mai cewa kamata yayi da wadanda suka zo yankin nan daga can nesan duniya da sunan tabbatar da tsaron yankin, su ne suka zamanto barazana ga tsaron yankin ba Iran ba.

Ministan tsaron na Iran ya kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da hakki da kuma karfin kare sararin samaniyarta, kasa da kuma ruwayenta. Don haka dakarun Iran ba za su taba bari wani yayi kokarin wuce gona da iri kan kasar su ba.

Ministan tsaron na Iran yana mayar da martani ne ga kalaman da jami'an Amurka suke yi dangane da atisayen da sojojin Iran suke yi a Tekun Fasha inda suka ce hakan yana a matsayin barazana ce ga yankin; lamarin da ya fuskanci kakkausar suka daga wajen Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran din Ayatullah Sayyid Ali Khamenei inda ya bukaci sojojin na Iran da su tabbatar wa da Amurka irin karfin da suke da shi a ruwayen Tekun Fashan don su dawo cikin hayacinsu.

Tags

Ra'ayi