Feb 18, 2016 16:20 UTC
  • An Fara Yakin Neman Zaben 'Yan Majalisu Dokoki Da Na Kwararru A Iran

A yau ne aka bude yakin neman zabe na 'yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran da kuma majalisar kwararru ta jagoranci ta kasar da za a gudanar a ranar 26 ga wannan wata na Fabrairu da muke ciki.

Kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) ya bayyana cewar tun da safiyar yau ne dai dubban 'yan takaran wadannan majalisu guda biyu suka fara yakin neman zaben bayan da Ma'aikatar cikin gida da kuma hukumar zabe ta kasar Iran din suka sanar da cewa an gama kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata a yi don fara yakin neman zaben a duk fadin kasar.

A bisa sanarwar da hukumar zaben ta bayar, akwai kimanin 'yan takara 6,200 da suka sanar da aniyarsu ta neman zaman 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar mai kujeru 290, kamar yadda kuma akwai wani adadi na 'yan takarar ma da suka tsaya don takarar kujerun majalisar kwararru ta jagoranci wacce ta ke da alhakin zabe da kuma sanya ido kan ayyukan Jagoran juyin juya hali na kasar.

Rahotanni dai sun ce tuni 'yan takarar suka fara yakin neman zaben wanda zai dauki mako guda ana yi. Gwamnati dai ta tanadi dubban wajaje da 'yan takarar za su mammanna hotuna da takardunsu na yakin neman zaben a duk fadin kasar don isar wa jama'a da abubuwan da suke son yi idan an zabe su.

Tags

Ra'ayi