Nov 25, 2016 05:51 UTC
  • Jiragen yakin kasar Amurka sun yi ruwan bama-bamai kan sansanin 'yan gudun hijrar Siriya

Mutane da dama sun rasa rayukansu sanadiyar ruwan bama-bamai da jiragen yakin kasar Amurka suka kai kan sansanin 'yan gudun hijrar Siriya.

Rahotanni dake fitowa daga jihar Rikka na arewacin Siriya  na cewa Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu sannan kuma wasu da dama na daban sun jikkata, sanadiyar wani hari ta sama da jiragen yakin Amurka suka kai kan mazugunin 'yan gudun hijra dake arewaciun garin Rikka.

Wannan hari dai na zuwa kwanaki uku bayan ruwan bama-baman da jiragen kawancen yakin da ta'addanci kalkashin jagorancin Amurka suka kai kauyen Salihiya dake arewacin garin Rikka, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 10 daga cikin su 6 iyalan gida guda ne.

Tun daga watan Agustan shekarar 2014 ne kasar Amurka da wasu kasashe masu goya mata baya suka kafa kungiyar yakar IS a Siriya, ita dai wannan kungiya an kafa ta ne ba tare da neman izinin Gwamnatin Siriya ba da kuma MDD, ya zuwa yanzu  kungiyar ta kashe fararen hula da dama tare da rusa gine-gine masu yawa a kasar ta Siriya.

Tags

Ra'ayi