Haramtacciyar kasar Isra'ila ta ce za ta dauki matakai na mayar da martani kan kisan sojojinta da wani bafaletine ya yi a cikin birnin Quds.

Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, a zaman da majalisar ministocin haramtacciyar kasar Isra'ila ta gudanar karkashin jagrancin Benjamin Netanyahu, ta yanke shawar daukar wasu kwararan matakai kan Falastinawa sakamakon halaka sojoji 4 da Fadi Ahmad Hamdan Kanbar ya yi.

Isra'ila ba ta bayyana matakan ba, amma tuni ta yi umarnin da a rushe gidan Fadi Ahmad, kuma ta kame danginsa da suka hada da mahaifansa da 'yan uwansa na jini, kuma ba a san halin da suke ciki ba, yayin da ake sa ido a kan falastinawa.

Jan 10, 2017 12:13 UTC
Ra'ayi