• Nuna Adawa Ga Shirin Trump Na Mayar Da Quds Babban Birnin Isra'ila

Jami'an gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Palastinawa sun yi kira ga larabawa da su nuna rashin amincewa da shirin Trump na mayar da birnin Quds a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila ta hanyar dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel aviv zuwa Quds..

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Shataya wani na hannun damar shugaban palastinawa Mahmud Abbas ya bayyana cewa, suna yin kira ga dukkanin al'ummomin larabawa da su mike domin nuna rashin amincewarsu da shirin da Donald Trump yake da shi, na mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Quds.

Inda ya ce suna kira da a ci gaba da gudanar da gangami da taruka a masallatai da majami'o'i a cikin kasashen larabawa, domin nuna wa Trump fushin al'ummar larabaw a kan wannan batun.

Ana sa ran a ranar 20 ga wannan wata na Janairu Trump zai sanar da dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel aviv zuwa birnin Quds, lamarin da zai tabbatar da amincewar Amurka da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra'ila a hukumance.

Jan 11, 2017 11:17 UTC
Ra'ayi