• Masar Ta Fara Sayen Man Fetur Din Iraki Maimakon Na Saudiyya

Daga lokacin da Saudiyya ta shigar da siyasa cikin sayar wa Da Masar man fetur, ta maye gurbinta da kasar Iraki.

Wani Jami'in Masar da ya bukaci a sakaya sunanshi ya ce; Daga lokacin da Saudiyya ta shigar da siyasa cikin sayar mata da man fetur, ta maye gurbinta da kasar Iraki.

Kamfanin Dillancin Labarun Spotnic na kasar Rasha ya ambato jami'in na ma'aikatar man fetur tana ci gaba da cewa; Wasu kasashen larabawa da na turai sun bayyana shirinsu na sayarwa da masar din man fetur don haka kasar za ta iya rusa yarjejeniyar da ta kulla da kamfanin Aramco na Saudiyya.

Bisa yarjejeniyar farko da Masar ta kulla da Iraki, a kowane wata kasar ta Iraki za ta rika bai wa masar ganga miliyan daya.

Sabanin siyasar da ya kunno kai a tsakanin Masar da Saudiyya ne ya sa Saudiyyar ta dakatar da bai wa Masar din man fetur da su ke da yarjejeniya akai.

Jan 11, 2017 19:12 UTC
Ra'ayi