• Yadda Kungiyar Da'esh Ke Shan Kashi A Mosul Na Iraki

A yayin da bayanai ke cewa jagoran kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh, Abou Bakr Al-Baghdadi ya tsere daga Mosul, kungiyar na ci gaba da rasa yankunan da take rikeda a wannan yankin na Mosul a Iraki.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da kuma kungiyar take fuskantar matsanancin matsin lamba daga dakarun gwamnatin Syria da sojojin kasar Rasha ke rufawa baya.

Hakan kuma na zuwa a daidai lokacin da ake hasashen Amurka zata aike da karin sojojin ta arewacin Syria domin dafawa mayakan Kurdawa dana larabawa a yakin da suke da kungiyar a birnin Raqa daya daga cikin sansanoni mafi girma na kungiyar ta Da'esh ko (IS).

Wasu bayanai da ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar sun nuna cewa kungiyar IS ta rasa kashi 65% na wuraren da  take rikeda idan aka kwatantan da lokacin da kungiyar ta bayyana sosai a shekara 2014.

Kana kuma bayanan sun ce an kashe kusan rabbin mayakan kungiyar.

A bayanan kuma da ma'aikatar ta Pantagone ta fitar sun ce kungiyar yanzu duk mutanen da take da basu wuce 15,000 ba.

A hannu daya kuma wani jami'in Amurka ya ce jagoran kungiyar Abou Bakr Al-Baghdadi y ajima baya jagorancin ayyukan ta'addancin da kungiyar ke aikatawa.

A Iraki, rundinar dake jagorancin yakin da akeyi a kasar ta sanar da cewa, dakarun yaki da ta'addanci sun kwato unguwar Moualemine dake yammacin birnin Mosul.

Yayin da sauren jami'an tsaron dake cikin farmakin da aka kaddamar tun a ranar 19 ga watan jiya domin kauto yankin yammaci, wanda shi ne birnin mafi girma a arewacin kasar ta Iraki.  

Saidai a halin yanzu rundinar bata bada izinin tunkarar tsohon gari ba inda keda jama'a sosai wanda kuma ake ganin fada a cikinsa zai yi wahala sosai.

Aman kafin hakan jami'an tsaron na farautar masu harbi daga nesa tare da zagaya sauren unguwannin domin tone nakiyoyin da 'yan ta'addan suka dasa, kamar yadda kwamandan rindinar kawo daukin gaggawa ta (FIR) kanal Abdel Amir al-Mohammedawi ya shidawa kanfanin dilancin labaren AFP.

A halin da ake ciki dai a cewar hukumar kula da bakin haure ta MDD cikin daririwan dubban fararen hula dake a birnin Mosul, dubu hamsin ne kawai suka samu tserewa domin isa sansanin 'yan gudun hijira.

Kungiyar IS dai na amfani da fararen hula a matsayi garkuwa na hana kai mata hare-hare.

Mar 10, 2017 06:00 UTC
Ra'ayi