Mar 14, 2017 17:23 UTC
  • An dai gudanar da zagaye har biyu a Astana ba tare da cimma wata matsaya ba kan rikicin Syria
    An dai gudanar da zagaye har biyu a Astana ba tare da cimma wata matsaya ba kan rikicin Syria

Yau Talata a sake komawa wani sabon zagayen tattaunawa a birnin Astana na kasar Kazakstan da nufin samar da mafita ga rikicin kasar Syria.

Saidai 'yan adawan kasar ta Syria da ake kiran masu sassaucin ra'ayin sun kauracewa tattaunawar ta yau, bisa abunda suka kira rashin mutunta matsayar da aka cimma kwanan baya ta dakatar da kai hare-hare.

Amman ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergio Lavrov ya ce rashin fahimtar juna aka samu akan halartar 'yan adawan a taro saboda wasu batutuwa da bangarori keda sabani a kai.

A nasa bangare kuwa shugaban tawagar gwamnatin Syria a tattaunawar, Bachar al-Jaafari, kalubalantar rashin halartar 'yan adawan ya yi a tattaunwa duk da a cewarsa rashin halartarsu ba zai hana a samu ci gaba ba.

An dai shafe zagaye har biyu a kasar ta Kazakstan a tattaunawar da kasashen Rasha da Iran da kuma Turkiyya ke jagoranta tare da goyan bayan MDD ba tare da cimma wata matsaya ba.

Rikicin Syria dai ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 320 a cikin shekaru shida.

Tags

Ra'ayi