Apr 29, 2017 05:47 UTC
  • Magabatan Bahrain Sun Hana Sallar Juma'a A Yankin Deraz

Watanni goma a jere da Dakarun tsaron Ali-Khalifa suke hana a gudanar da sallar Juma'a a yankin Deraz da suke ci gaba da killa ce shi.

Kamfanin dillancin Fars na kasar Iran ya habarta cewa A jiya Juma'a Dakarun tsaron Ali Khalifa sun hana Al'ummar musulmi mabiyar tafarkin Ahlulbait (a.s) tsaida sallar juma'a a Masallacin Imam Sadik (a.s) dake yankin Deraz da ya kwashe sama da watanni goma a killace  lamarin da ya Tilasta musu gudanar da sallarsu daidai ku.

Tun daga ranar 17 ga watan Yunun shekarar 2016 da ta gabata ce, aka dakatar da tsaida sallar juma'a a masallacin Imam Ja'afaru Sadik dake yankin Deraz na kasar Bahrain, kuma ko wani maku Dakarun tsaron masarautar Ali Khalifa na hana Limamin Juma'a da Mutane gudanar da sallar Juma'a a wannan masallaci.

A bangare guda, masu rajin kare hakin bil-adama sun bayyana rashin jin dadin su kan ci gaba da tsare Nabil Rajab  daya daga cikin masu rajin kare hakin bil-adama na kasar Bahrain a Kadaitaccen kurkuku , da kuma yadda kasashen Birtaniya da Amurka suka ja bakunan su suka tsuke kan yadda ake ci gaba da take hakin bil-adama a kasar ta Bahrain.

Tags

Ra'ayi