• Yemen: Dakarun Yemen Sun Kai Wa Sansanonin Sojan Saudiyya Hari.

Mayakan Ansarullah na kasar Yemen, sun maida martani akan sansanonin sojojin Saudiyya da ke Gundumomin Asir da Najran.

Mayakan Ansarullah na kasar Yemen, sun maida martani akan sansanonin sojojin  Saudiyya da ke Gundumomin Asir da Najran.

Majiyar  mayakan na Ansarullah ta ci gaba da cewa; Harin sun kai shi ne a garuruwan Sudaisi da sakam da almakhruq, da makamai masu linzami samfurin katusha.

Hare-haren na dakarun Yemen din dai suna a matsayin maida martani ne akan wuce gona da irin da Saudiyyar ta ke yi akan al'ummar Yemen.

fiye da mutane dubu 12 ne Saudiyyar ta kashe a cikin kasar Yemen, tare da jikkata wasu dubban kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ambata.

Jun 18, 2017 11:56 UTC
Ra'ayi