Jun 18, 2017 15:45 UTC
  • Wani Harin Sama Ya Kashe Fararen Hula 24 A Yemen

Rahotanni daga Yemen na cewa a kalla mutane 24 ne suka ras arayukansu a wani harin sama da aka kai kan wata kasuwa dake wani yankin 'yan shi'a a kusa da iyaka da Saudiyya.

Harin wanda aka alakanta dana kawacen kasashen Larabawa da Saudiya ke jagoranta an kai shi ne kasuwar saida wani ganye da ake kira Qat wanda 'yan Yemen ke yawan amfani da shi.

Wasu da suka shaidi lamarin sun ce sun ganewa idanunsu gawarwaki da dama wadanda harin ya kona kurmus.

Kawacen da Saudiya ke jagoranta a kasar Yemen kan 'yan Houtsis don goyan bayan gwamnatin Yemen mai murabus an jima ana zarginsa da kashe fararen hula bisa kuskure.

 

Tags

Ra'ayi